Gwamnatin Tarayya Ta Umarci Ma’aikata Su Koma Bakin Aiki

Gwamnatin tarayya ta umarci ma’aikatan gwamnati da ke aiki daga gida tun watan Maris saboda korona su koma aiki ranar Litinin 19 ga watan Oktoba.

Shugaban kwamitin Shugaban Ƙasa na Yaƙi da Korona, PTF, Boss Mustapha da jagora na ƙasa, Sani Aliyu ne suka sanar da haka yayin taron manema labarai ranar Talata.

Ma’aikatan gwamnati na mataki 12 zuwa sama da waɗanda ke yin ayyuka masu matukar muhimmanci ne suke zuwa aiki.

Amma a yanzu kwamitin ya umurci dukkan ma’aikata na ƙasa da mataki na 12 su koma bakin aiki. Amma duk da haka ta umarci ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin da ke karkashin gwamnati su raba ranakun da ma’aikatan za su rika zuwa aiki don gudun cinkoso.

Labarai Makamanta

Leave a Reply