Ƙaramin ministan ilmin Najeriya, Hon. Chukwuemeka Nwajiuba, ya yi kira ga ‘yan kungiyar malaman jami’a ASUU babu dole a batun karantarwa, su shiga harkar noma kawai.
Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana cewa ana bukatar karin manoma, don haka malaman makarantar na iya rabuwa da aji, su koma gona, domin ƙara adadin manoma a ƙasar.
Ministan ilmin ya kuma yi bayani game da shirin da gwamnati ta ke yi na bude makarantu, ya ce za a rika yin darusa da rana da nufin rage cunkoso. Nwajiuba ya bayyana haka ne lokacin da aka gayyace shi a gidan talabijin na Arise News a Abuja.
A game da dogon yajin-aikin kungiyar ASUU, ministan ya ce dama can ba saboda annobar COVID-19, malamai su ka rufe jami’o’in Najeriya ba. Don haka ya bada shawara ga malaman jami’o’in kasar da su yi tunanin komawa noma saboda gwamnati ta na bukatar karin manoma a halin yanzu.
Mai girma Ministan ya ke cewa ASUU ta na da damar da za ta mikawa gwamnati kokon bararta, amma ya ce an biya malamai albashi har zuwa Yuli.
“Ba su fara yajin-aiki a kan COVID-19 ba. Dama can ASUU ta na yajin-aiki kafin zuwan annobar COVID-19.” Inji Karamin Ministan.
“Ana daf da za a rufe makarantu, (ASUU) su ka tattara su ka tafi yajin aiki.
“Gwamnati ba ta tsare kowa ba. Cewa ta yi idan zan biya ku, dole ya zama ta tsarin IPPIS. Za ka iya barin aikin, ka tafi idan ka ce ba za ka yi ba.” Ministan ya cigaba da karin bayani, ya na cewa: “Ba na son in koyar. Za ka iya samun wani abin yi. Abin da mu ke bukata a yanzu sosai su ne manoma.”