Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya sanar da ranar bude makarantun tarayya a fadin kasar. Za’a bude makarantun ranar 11 ga watan Octoba na wannan shekara ta 2020.
Wannan na kunshe na a wata wasika da Ministan ya sanyawa hannu kuma aka rarrabawa manema labarai ranar Laraba a garin legas.
Sai dai bude makarantun zai shafi dalibai yan makarantar sakandare ne kawai.
Adamu Adamu yace anyi hakane domin aba daliban da suka dade zaune a gida damar kammala zangon karantunsu wanda zai kare karshen Disamba.
Ministan ya bada shawara akan abi ka’idojin kare kai daga cutar Covid-19 a makarantun domin takaita yaduwar ta tsakanin dalibai.
“Har ila yau, Makarantun da basu kammala zangon karantunsu na biyu ba suyi kokari su kammala sannan su shiga zangon karatu na uku wanda ake sa ran zai kare a watan Disambar 2020, “A cewar shi.