Gwamnatin Tarayya Ta Roki Gwamnoni Su Tabbatar Shinkafar Da Aka Basu Ta Kai Ga Talakawa

IMG 20240708 WA0041

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu ta yi kira ga gwamnonin Jihohi su tabbatar shinkafar da aka basu takai ga hannun talakawa.

Mnistan yaɗa labarai Alhaji Mohammed Idris ne ya yi wannan kiran a Abuja, lokacin da yake karin haske dangane da matakan da gwamnatin Tinubu ke ɗauka na magance matsalar yunwa dake addabar ‘yan ƙasar.

A ranar Litinin ɗin wannan mako ne gwamnatin tarayya ta sanar cewa ta bai wa gwamnoni tirelolin shinkafa waɗanda za su raba wa al’umma domin rage raɗaɗin yunwa.

A lokacin da ya yi bayani bayan taron ɓangarren zartaswa na gwamnatin tarayya, ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ya ce an bai wa kowace jiha haɗi da Abuja tirelar shinkafa 20 domin raba wa talakawa.

Ya ce kowace tirela tana ɗauke da buhun shinkafa 1,200 kg25 da aka ba gwamnonin jihohi a wani mataki na rage wa talakawa raɗaɗin ƙarancin abinci da tsadarsa da ake fuskanta a ƙasar.

Gwamnatin Tarayya ta ce tana fatan gwamnonin jihohin za su raba kayan abincin ga mabuƙata a matakin jiha da ƙananan hukumomi.

Hakan na nufin kowace jiha, da kuma babban birnin tarayya za ta samu jimillar buhunan shinkafa masu nauyin 25kg guda 24,000.

Ana dai fama da tsadar kayan abinci da ake alaƙantawa da matsalolin tattalin arziki wanda janye tallafin mai da matsalar tsaro suka haddasa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply