Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Cibiyar Daƙile Bazuwar Makamai

Shugaba Muhammdu Buhari ya amince a kafa Cibiyar Dakile Bazuwar Manya da Kananan Makamai. Mashawarci a Bangaren Tsaro, Babagana Monguno ne ya bayyana haka, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Wannan sabuwar cibiya idan an kafa ta, za ta kasance a karkashin Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Tsaro. Haka dai Monguno din ya shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Kasa.

Ya kara da cewa cibiyar za ta kasance irin Cibiyar Dakile Ta’adanci, wadda ita din ma a karkashin kulawar sa ta ke.

Ya ce idan aka kafa cibiyar, za ta yi aiki ne a bisa ka’idojin da kasahen duniya da kuma ECOWAS suka gindiya dangane da batun dakatar da bazuwar makamai.

Ya kuma kara yin bayani cewa cibiyar za ta hana safarar makamai tare da tattara dimbin makaman da aka kama ana lalata su.

Shugaba Buhari ya amince da kafa cibiyar ce bisa shawara ta. Kuma za ta kasance a karkashin kulawar ofishi na, na Mashawarci a Bangaren Tsaro.” Cewar Moguno.

Labarai Makamanta

Leave a Reply