Gwamnatin Tarayya Ta Janye ?arin Farashin Kudin Lantarki

Ma’aikatar da ke kula da harkokin wutar lantarki ta ?asa ta dakatar da wani ?arin ku?in wuta da aka yi, bayan barazanar da kungiyoyin ?wadago suka yi na sa-kafar-wando-guda da gwamnati.

A wannan makon ne aka sanar da ?arin farashin, wanda mahukunta suka danganta da hauhawar farashi, inda kilowatt ?aya ya tashi daga naira biyu ya koma naira hu?u.

Ma’aikatar wutar ta hanzarta sanar da janye karin ku?in wutar da aka yi ne, kamar yadda ta ce domin ta fahinci cewa an jahilci ?arin, saboda wasu na cewa ya kai kashi hamsin cikin ?ari, alhali, ?arin yana da nasaba ne da hauhawar farashi, kuma doka ce duk bayan wata shida, hukumar da ke kula da harkokin wutar lantarki da sauran ?angarorin da abin ya shafa, kan yi nazarin halin da ake ciki domin daidaita ?arin da ya dace.

Mai taimaka wa ministan wutar lantarki Injiniya Sale Mamman kan hulda da jama’a Ado Adamu ya ce gwamnati ta dakatar da ?arin ne ganin cewa akwai tsohuwar jayayyar da ?ungiyar ?wadago ke yi da gwamnati dangane da wani tsohon ?arin farashi da ba a cim ma maslaha ba tun watan Satumban bara.

Tun lokacin da maganar karin kudin wutar ta fito, ?ungiyar ?wadago da wasu dangoginta da ke fafutukar kare ha??in masu amfani da wutar lantarkin suka yi ta kumfar-baki, suka fara ta da ?ura.

Related posts

Leave a Comment