Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya ce gwamnatin tarayya ta gaza a bangaren mai da kuma iskar gas, inda ya ce ya kamata ta fice daga bangaren kasuwancin.
El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin taron zuba jari da hukumar karfafa zuba jari ta jihar Kaduna ta shirya.
Gwamnan ya ce bangarori da ke aiki a wannan kasa kamar bangaren nishadi da harkar sadarwa da kuma fasaha da sauransu, gwamnati ba ta da hannu a cikinsu.
A cewarsa, babu wani abu da ya sauya tun bayan cefanar da babban kamfanin man fetur na Najeriya a watan Yulin 2022.
Ya kara da cewa duk da irin kokari da shugaban kamfanin na NNPC Mele Kyari yake yi, kamfanin ya gaza a bangaren kasuwancin mai.
“NNPC babbar matsala ce ga Najeriya wacce ta fi karfin mutum daya wanda muddin ba a shawo kan matsalar ba, to za ta iya durkusar da Najeriya,” in ji El-Rufai.