Gwamnatin Tarayya Ta Dage Gudanar Da Aikin Kidaya

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana gwamnatin tarayya ta ɗage aikin ƙidayar jama’a da ta shirya fara gudanarwa ranar 29 ga watan Maris zuwa watan Mayu mai zuwa.

Ministan yaɗa labaran ƙasar Lai Mohammed ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwar ƙasar da shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya jagronta a Abuja fadar gwamnatin ƙasar.

Lai Mohammed ya ce matakin ɗage aikin ƙidayar ya zama wajibi ne bayan da hukumar zaɓen ƙasar ta ɗage zaɓukan gwamnoni zuwa ranar 18 ga watan Maris, a maimakon ranar 11 ga watan kamar yadda aka tsara gudanar da shi a baya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply