Gwamnatin Tarayya Ta Biya ASUU Albashin Rabin Wata

Gwamnatin tarayya ta biya Malaman jami’a dake karkashin kungiyar malamai masu koyarwa ta ASUU albashin kwanaki 18 na watan Oktoba, domin rage musu radadin rashin albashi na tsawon watanni takwas da suka shafe suna yajin aiki.

Malaman jami’o’i da dama da Wakilinmu ya tuntuba sun tabbatar da hakan inda suka ce an biya su rabin albashinsu ne kuma yana nuna na watan Oktoba ne.

A bayanin da wani malamin jami’a yayi wa wakilinmu yace ya samu albashin babu zato balle tsammani duk da cewa ba wannan bace yarjejeniyar dake tsakaninsu da gwamnatin tarayya ba. ”Na samu Albashin wurin karfe shida na yammacin Alhamis, 3 ga watan Nuwamban 2022.

Rabonmu da jin shigowar albashi tun a wata Fabrairu. ”Ba zan ce ina ɗokin kudin ba saboda tuni na gane cewa ba zan iya rayuwa a kan albashina ba. Shiyasa na kama wasu ayyukan tun kafin ma a tafi yajin aiki.“

Ita kuwa Malama Fatima Bello, tace ta matukar jin dadin shigowar wannan Albashin tunda dama iya wahala sun dandana. ”Daga ni har mijina malaman jami’a ne, idan nace wannan watannin da muka kwashe babu albashi nayi su cikin walwala, gaskiya nayi karya.

”Amma kuma wannan zan iya cewa ya zama darasi gareni da ire-irena da suka riki koyarwa a jami’a matsayin aikin yi daya tak. ”Yanzu ina fatan su kammala biyanmu in tada jari mai tsoka saboda halin ko ta kwana.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply