A madadin Gwamnatin tarayyar ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar da sanarwar hutun ta bakin Ministan harkokin cikin gidan Mista Rauf Aregbesola.
Gwamnatin ta ayyana tarar Jumaa 25, da ranar Litinin 28 na wannan watan na Disembar 2020 a matsayin ranakun hutun Kirsimiti.
Har ila yau hutun ya hadar da ranar Jumaa 1, watan Janerun Shekarar 2021, don murnar sabuwar shekarar, inji Rauf.
A madadin Ministan, sakataren dindindin na maaikatar harkokin cikin gidan Dakta Shuaib Belgore, ne ya tabbatar da hakan yau laraba, sun yi kira ga mabiya Addinin Kirista da suyi bukukuwan su bisa bin doka da odar masana don kucewa yaduwar Cutar Corona Virus.