Gwamnatin Tarayya Ta Bada Umarnin Bude Kamfanin Simintin Dangote A Jihar Kogi

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umurnin sake bude kamfanin simintin Dangote na Obajana da ke jihar Kogi.

Hakan ya fito yayin taron majalisar tsaro da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar juma’a a fadarsa dake Abuja.

Ministan harkokin ‘yan sanda, Mohammed Dingyadi da takwaransa na harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola wadanda suka kasance a taron, sun shaida wa mana labarai cewa an cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Kogi da kuma kamfanin Dangote.

Aregbesola ya bayyana cewa bangarorin biyu sun amince na sake bude kamfanin simintin na Obajana, inda aka bukaci dukkansu da su mutunta yarjejeniyar.

Ministan ya kuma kara da cewa majalisar ta amince cewa za a warware dukkan batutuwa da suka janyo sabani tsakanin bangarorin saboda a cewarsa gwamnati na da zummar samarwa mutane aikin yi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply