Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Fara Aikin Titin Dogon Kaduna Zuwa Kano

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana wa manema labarai cewa Gwamnatin Tarayya ta biya dala miliyan 218, matsayin somin-taɓin fara aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano.

Amaechi ya bayyana haka yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja.

Ya ce tantagaryar adadin kuɗaɗen kwangilar dala biliyan 1.2 ne. Amma daga cikin an fara biyan dala miliyan 218, domin a fara aikin titin cikin wannan wata na Yuli da mu ke ciki.

Amaechi ya ce yanzu hankalin gwamnatin tarayya ya karkato a kan aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano, tunda an rigaya an kammala na titin Legas zuwa Ibadan.

“A yanzu abin da ya rage a biya kudin aikin su ne dala miliyan 900. Kuma nan da makonni kaɗan masu zuwa za a sake biyan dala miliyan 100.” Inji Amaechi wanda ya ce ya na sa ran zuwa ƙarshen wannan shekara za a yi ƙoƙari a biya dala miliyan 600.

Ya kuma yi magana kan sauran titinan da Gwamnatin Tarayya ta ƙudidi aniyar shimfiɗawa, kuma duk na jirgin ƙasa daga na Maiduguri da na Ibadan zuwa Kano, da na Legas zuwa Calabar.

Ya ƙara da cewa an fara biyan kuɗin somin-taɓin aikin titin jirgin ƙasa na Kano daga Kaduna daga cikin kasafin gwamnatin tarayya.

“Akwai kuma sauran kashin kuɗaɗen wanda China ce za ta biya, amma ba ta fara biyan ba tukunna.

“Kada ku tambaye ni inda Najeriya ta samu kuɗin da ta biya. Domin a matsayi na na Kirista, gidan Shaiɗan ne kaɗai ba zan iya zuwa neman bashi ba.” Inji Minista Amaechi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply