Gwamnatin Tarayya Ta Amince Za Ta Ba Malaman Jami’o’i Kuɗaɗen Alawus

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince za ta biya Naira biliyan 30 kudin allawus na malaman da ke koyarwa a jami’o’in kasar. Sai dai ba lokaci guda gwamnatin za ta biya kudin ba inda ta ce za ta biya daga watan Mayun 2021 zuwa Fabrairun 2022.

An ruwaito cewa gwamnatin tarayyar ta yi alkawarin kashe Naira biliyan 20 domin farfado da fanin ilimi a kasar yayin tattaunawar da suka yi don ganin an kawo karshen yajin aiki da kungiyar malaman jami’o’i ASUU ta yi watanni bakwai tana yi.

Wadannan na daga cikin yarjejeniyar da aka cimma wurin tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’i’i wato ASUU a ranar Alhamis.

Tunda farko kafin ya shiga taron, Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige ya ce rufe makarantun da ASUU ta yi ne ya ingiza dalibai shiga zanga-zangar #EndSARS da matasan suka kwashe kwanaki suna yi.

Ngige da karamin ministan sa Festus Keyamo (SAN) ne suka jagoranci tawagar gwamnati yayin da Farfesa Biodun Ogunyemi, shugaban kungiyar ASUU ya jagoranci malaman jami’an.

Labarai Makamanta

Leave a Reply