A yau Alhamis gwamnatin tarayya ta amince a bude makarantu. Inda tuni jijohin Lagos, Ondo, Kogi da sauransu suka soma shirin bude makarantu a cikin wannan wata.
Haka kuma gwmnatin ta amince a bude sansanonin horas da yi wa ƙasa hidima (NYSC). Ta kuma sassauta dokar hana zirga zirga zuwa karfe 12am – 4am. Tare da amincewa a dawo da zirga zirga ta sufurin jiragen sama.
Ɗaliban makarantu a Najeriya dai sun lashe kimanin watanni shida suna zaune a gida, tun bayan sanar da ɓullar cutar sarƙewar numfashi ta CORONA.
Ana sa ran hukumomin makarantun za su bi dokoki da ƙa’idoci na Hukumar daƙile yaɗuwar cututtuka ta ƙasa wato NCDC ta hanyar ba da tazara sanya takunkumi da wanke hannu.