Gwamnatin Taraba Ta Ci Mutuncin ‘Ya’yan Kungiyar Mu _ Masu Hakar Ma’adinai

BASHIR ADAMU, JALINGO.

Rahotannin dake shigo mana yanzu daga Jihar Taraba na cewa Kungiyar Masu Hakan Ma’adinai ta Kasa, Shiyyar Arewa Maso-Gabas ta zargi Gwamnatin Jihar Taraba ta hannun Kwamitin Kula da Hana Tonan Ma’adinan Kasan Jahar, karkashin jagorancin, Janar Jeremiah Faransa (mai ritaya) da kama musu a kalla membobi 3,500 tare da tozatar dasu, da kwace Gwalagwalansu na Miliyoyin Naira a Karamar Hukumar Tongo na Jihar Adamawa.

Sakataren Kungiyar na Shiyyar Arewa Maso Gabas, Kwamarade Salisu Shu’aibu Mai-zare yayi zargin a wurin wani taron Manema labarai da ya kira a Jalingo fadan Gwamnatin Jaha.

Shu’aibu Mai-zare yace sunyi mamakin yanda za’ace tsohon Janar na Sojin Nageriya ya jagoranci Kwamitin da zasu afkama membobinsu a wata Jaha ta daban da aka umur cesu dayin aiki.

“Mun kira ku ku yan-jaridu ne a yau, don ku sanar da Duniya irin cin mutuncin da Kwamitin Hana Tonan Ma’adinai ta Jihar Taraba tayimana, muna Allah Wadai, kana muna kira ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu daya gaggauta shiga tsakanin wannan lamari.

“Dole a sakomana Membobinbu ba tare da gindaya wani sharadi ba.

“Wadanda aka kama, akaci zarafinsu halastattacen aikinsu sukeyi a cikin Gundumar yankin ‘Mbagi Kolo’ na Karamar Hukumar Tongo ta Jihar Adamawa. Kuma Kamfani mai Lasisi sukeyima aiki, cikin Ka’ida da bisa umurnin mamallakin Filin da ake aikin, da sanin Dagacin Yankin, Karamar Hukumar Tongo da Jihar Adamawa.

“Hanyar shiga yankin ne akebi ta ‘Kauyen Dogon Yatsu, dake Karamar Hukumar Bali ta Jihar Taraba.

Mai-zare ya kuma tunatar da cewa ayyukan da sukeyi ko shakka babu na tallafawa Gwamnatoci samun kudin shiga, samar da ayyukanyi ga matasa da rage ayyukan ta’addanci da kawo cigaban Kasa baki daya.”

Sai dai kuma, Shugaban Kwamitin Hana Hakan Ma’adinai na Jihar Taraba, Janar Jeremiah Faransa (mai ritaya) yace su basu shiga Jihar Adamawa ba, a Kauyen ‘Dogon Yatsu’ dake Karamar Hukumar Bali ta Jihar Taraba ne suka gudanar da aikin su.

Labarai Makamanta

Leave a Reply