Gwamnatin Kaduna Ta Fara Bi Gida-Gida Domin Dawo Da Kayan Tallafin Da Aka Sace

Gwamnatin jihar Kaduna ta fara bi gida gida domin gano kayayyakin tallafin COVID-19 da aka sace a dakin ajiyar kayan da ke wasu garuruwa na jihar.

Rundunar ‘yan sanda tare da sauran jami’an tsaro ne za su fara wannan atisayen binciken gida gida don gano kayan tare da cafke wadanda aka kama da laifin satar su.

Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufa’i ya tabbatar da wannan atisayen a shafinsa na Twitter a ranar Talata.

Ya zuwa yanzu, rahotanni suna ta bayyana yadda bata gari ke ci gaba da fasa shaguna da dakin ajiyar kayan tallafi da ma na ‘yan kasuwa, inda suke wawushe komai.

Ofishin hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, a jihar Kaduna, na daga cikin wuraren da bata garin suka kaiwa farmaki a jihar. Baya ga satar kofofi da kayan ofis ofis, bata garin sun yi awan gaba da “masu hatsari kuma miyagun” magunguna, a cewar gwamnatin jihar.

A yayin da ya ke karin haske a wani jawabin, El-Rufai ya ce gwamnatinsa ta yanke hukuncin hukunta duk wanda ya saci kayan gwamnati ko na jama’a. Ya ce gwamnati ba za ta lamunci sata da lalata kaya jama’a a jihar ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply