Gwamnatin jihar Kaduna ?arkashin jagorancin Gwamna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i ta fallasa inda miyagun ‘yan bindiga da suka addabi jihar ke samun kudaden shiga.
Daga cikin hanyoyin samun kudinsu kamar yadda gwamnatin jihar tace, shi ne wurin karbar kudin fansa daga ‘yan uwan wadanda suka sace, da sauran cuwa cuwa da kayayyakin Haram.
Wannan na kunshe ne a rahoton tsaro na watanni uku da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya mika wa gwamnatin jihar kuma Jaridar Daily Trust ta samu kwafi.
Rahoton ya lissafo sauran hanyoyin da kudi ke shigo musu da suka hada da siyar da dabbobin sata, ribar cinikayyar makamai da kuma bayar da hayar makamai ga wasu kungiyoyin ta’addanci.
“Wasu kungiyoyi na bayar da hayar makamai ga kungiyoyin da basu da shi kuma su raba kudin da suka samu wurin ta’addanci.” Sauran hanyoyin samun kudin sun hada da harajin dole da suke kallafa wa manoma a kan gonakinsu.
Rahoton ya kara da bayyana cewa, su kan bai wa masu kai musu bayanan sirri jari domin kasuwanci wanda suke aike musu da ribar. Ya kara da bayyana yadda ‘yan bindigan ke kashe kudin ta hanyar siyan bindigogi, makamai da abinci.
Sauran sun hada da kudaden kaiwa da kawowa, magani, siyan kayan shaye-shaye, biyan masu kai musu bayanan sirri, kafafa kasuwanci wanda masu kai musu bayanai ke yi da kuma kai wa bokaye kudi domin nasarar aiyyukansu.