Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Gwamnatin Kaduna Ta Dauki Matakin Hana Gudanar Da Duk Wata Zanga-Zanga A Jihar

IMG 20240310 WA0186

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa Gwamna Uba Sani ya fara ɗaukar matakai da nufin hana zanga-zangar da ake shirin yi a watan Agusta mai zuwa.

Sanata Uba Sani ya gana da shugabannin hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya, da roki matasa gami da wayar da kan mutane kan illar zanga-zanga

Ya ce masu shirya wannan zanga zanga suna da wata ɓoyayyar manufa ta tayar da tarzoma da gurgunta kasuwancin ƴan ƙasa.

Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne yayin da matasa ke shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin kasar nan kan tsadar rayuwa da yunwar da ake ciki.T

Taron dai an yi shi ne domin inganta tsaro a manyan yankunan Kaduna da kuma wayar da kan mutane game illar yin zanga-zangar da za a yi, Arise TV ta ruwaito.

Gwamna Uba Sani ne ya jagoranci taron wanda ya gudana a gidan gwamnati Sir Kashim Ibrahim da ke cikin birnin Kaduna ranar Jumu’a.

Uba Sani ya caccaki masu shirya zanga-zangar inda ya ce duk da ba a san fuskokin su ba amma alamu sun nuna suna ƙoƙarin tayar da tarzoma ne a ƙasar nan. Ya kuma yi zargin cewa an shirya zanga-zangar ne da nufin cimma wata manufar siyasa da tada hankalin al’umma don sace masu kayan sana’o’insu.

Ya kuma sha alwashin cewa gwamnatin jihar Kaduna da al’umma ba za su goyi bayan duk wata zanga-zangar da manufarta ita ce tada rikici da cutar da jama’a ba.

A cewar gwamnan, babu buƙatar wannan zanga-zangar da ake shirin yi domin ɓa za ta amfani jihar Kaduna ko ta kawo waraka a Najeriya ba, Murya Yanci ta kawo.

Don haka Gwamna Sani ya shawarci sarakuna su wayar da kan jama’arsu kan illolin da ke tattare da shiga zanga-zangar da ka iya tada zaune tsaye a kasar nan.

Ya kuma ba su tabbacin cewa gwamnatin Kaduna ba za ta yi ƙasa a guiwa ba a ƙoƙaren share hawayen al’ummarta musamman saboda halin kuncin da aka shiga.

Exit mobile version