Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasir Erufai ta bayyana kwanaki uku a matsayin ranakun ci gaba da nuna alhinin rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.
A takardar da gwamnatin Kaduna ta sanar da hakan, ta bayyana cewa duk da nuna jimamin za a bude ofisoshin gwamnati a ranakun Litinin da Talata, amma za a yi hutun gama gari a ranar Laraba.
Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya ce jama’ar jihar Kaduna sun yi babban rashi. Ya mika godiyarsa ga shugaban kasar a kan tura wakilansa da yayi domin halartar jana’izar.
Manyan kasa da dama sun aike da ta’aziyya dangane da wannan babban rashi da aka yi.
A saƙon ta’aziyar shi Shugaban gidajen rediyo da talabijin na Liberty Alhaji Tijjani Ramalan ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin wani rashi da ya shafi ƙasa baki ɗaya, wanda har abada ba za’a manta da shi ba.
Shima tsohon gwamnan jihar Kaduna Alhaji Ahmed Maƙarfi ya bayyana rasuwar ta Sarkin Zazzau a matsayin wani rashi da jarrabawa da ta faɗo wa jihar Kaduna, inda yayi addu’ar Allah ya jiƙanshi ya gafarta mishi.
Babban Malamin addinin musulunci Sheikh Dr Ahmad Gumi a sakon ta’aziyar da ya bayar, ya yi addu’ar neman gafara da samun rahama ga marigayi Sarkin, wanda ya bayyana shi a matsayin abin koyi.
Ita ma a sakon ta’aziyar da ta gabatar, tsohuwar shugabar ƙaramar Hukumar Lere kuma tsohuwar ‘yar majalisar dokokin tarayya Hajiya Saudatu Sani, tace wannan rasuwa ta Sarkin na Zazzau ta yi matukar girgizata, sannan ta yi addu’ar neman gafara a gareshi.
Marigayi Sarkin Zazzau shine Sarki na 18 na Fulani a masarautar Zazzau. Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.
Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa, basaraken ya rasu a asibitin 44 da ke Kaduna wurin karfe 11 na safiyar Lahadi.
Ya kwanta rashin lafiya tun a ranar Juma’a kuma an kai shi asibiti inda ya rasu.
Tuni dai aka yi jana’izar shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a birnin Zazzau, muna addu’ar Allah ya jiƙanshi ya gafarta mishi Allahumma amin.