Gwamnatin Edo Ta Rushe Masallaci Da Kasuwar ‘Yan Arewa

Labarin dake shigo mana daga Jihar Edo na cewa gwamnatin jihar na ci gaba da rusa matsugunan ‘yan Arewa.

BBC ta ruwaito cewa wuraren da aka rushe a ranar Talata su ne yankunan da ‘yan arewa suke da gagarumin rinjaye a yankuna daban-daban.

‘Yan Arewa mazauna jihar Edo dai sun zargi jami’an gwamnatin jihar da rushe wata kasuwa da wani Masallaci da ke yankin da galibinsu suke zaune.

Sai dai gwamnati ta ce rusau din ba shi da nasaba da addini ko kabilanci, tana mai cewa ta dauki matakin ne domin dakile matsalolin tsaro da ke addabar jihar.

Related posts

Leave a Comment