Gwamnatin Delta Ta Janye Aniyarta Na Korar ‘Yan Arewa Daga Jihar

A yanzu haka dai hankalin ‘yan arewacin Najeriya mazauna garin Abavo da ke jihar Delta ya kwanta, biyo bayan janye wa’adin da ake zargin masarautar garin ta ba su na kwanaki hudu da su fice daga garin, saboda yawaitar matsalar sace-sacen jama’a da ta addabi yankin.

Janyewar wannan wa’adi dai ta biyo bayan kwarmata lamarin da ‘yan arewar suka yi a sashen Hausa na BBC, abin ya kai ga kunnen fadar shugaban Najeriyar, da gwamnan jihar ta Delta, da shugaban ?aramar hukumar Ika ta Kudu, da Ha?akar ?ungiyoyin kare fararen hula na arewacin Najeriya ta CNG, na shiga tsakani.

Sarkin Hausawan garin na Abavo, Usman Alasan ya shaidawa BBC cewar “mun yi sallah lafiya ranar juma’a babu wanda ya ce mana kanzil, gwamnan jihar ya turo mana wakilai don jin halin da muke ciki, sannan aka tura DPO ya je wajen sarakunan yankin, inda kuma ya dawo ya sanar da su cewar an janye wannan wa’adi da aka ba su”

Sarkin Hausawan garin na Abavo ya ce “Dukkan ?angarorin an yi kira garesu tare da jan hankalinsu da dukkan su zauna da juna lafiya ba tare da wata fargaba ba” inji shi.

”Babu wani sharadi da aka shimfida mana na ci gaba da zama a garin, muna ci gaba da jan hankalin Hausawan da ke yankin da su ci gaba da kiyaye doka da oda, kar su ?ata mana suna, sannan su ci gaba da kasuwancinsu, tunda babu wani sharadi ko matakai da aka gindaya mana” Inji Sarkin Hausawan.

A makon da ya gabata ne hankalin al’ummar arewacin ?asar da ke zaune a garin Abavo da ke jihar Delta, yake a tashe, sakamakon wa’adin kwanaki hu?u da ake zargin masu garin sun ba su, na barin garin, kan yadda ake satar mutane a yankin.

Sai dai a yayin wata hira da BBC, Sarkin Hausawan garin Usman Alhassan ya ce lamarin ya dama lissafin wasu daga cikinsu, saboda yadda suke fama da ku?in cin abinci bare ta mota, kuma wa’adin kwana hu?u da suka basu ya yi ka?an.

Sai dai wani ?an majalisar masarautar garin na Abavo ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin,” sai dai ya ce an ?auki matakin ne don yawaitar sace-sacen mutane don neman ku?in fansa, da sauran maganganu da ya ce lokacin fa?arsu beyi ba sai wani lokaci.

Related posts

Leave a Comment