Gwamnatin Buhari Ce Ta Samar Da ‘Yan Bindiga – Obasanjo

Rahotannin dake shigo mana daga birnin Abeokuta na jihar Ogun na bayyana cewar tsohon Shugaban ?asa Cif Olusegun Obasanjo yace Najeriya na bukatar Jarumin shugaba wanda zai yi aiki babu sani babu sabo.

Obasanjo ya ce Najeriya na bukatar shugabanni wa?anda za suyi tu?uru ta kowace fuska tamkar masu ?an ta?in hankali da za su iya mai da kasar kan turba mai dorewa.

Obasanjo ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin ?an takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Mohammed Hayatu-Deen a gidan sa.

Ya nuna ?acin ransa kan halin da Najeriya ke ciki ba na koma baya da ta?ar?arewa mafi muni a tarihin kasar karkashin jagorancin Buhari.

Tsohon shugaban ya jaddada “Ku daina cewa Allah ne ya kawo matsalar da muke ciki Gwamnatin Buhari ce ke da alhakin ‘yan Bindiga da masu satar mutane”.

Obasanjo ya bayyana cewar Najeriya za ta iya kawo karshen matsalar tsaron da take fama da ita cikin shekara biyu in ta samu shugaban da ya dace wanda kuma yake fatan daukar matakan da suka dace.

Related posts

Leave a Comment