Daga Wakilinmu
A kokarinsu na ganin sun samarwa da Matasa ayyukan yi, Gwamnatin Jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Zulum, da hadin gwiwar kamfanin hada hadar kudi irin na zama ni, wato Bizi Mobile Cashless Consultant limited, da kamfanin Kama Integrated Services limited da kuma BRMFB, sun horar da Matasan Jihar Borno Maza da Mata har su kimanin 270 harkar Agency Banking da kuma basu horo na musamman akan shirin Babban bankin kasa (CBN) akan harkar e-Naira.
Taron horarwar na musamman wanda aka shirya shi na yini biyu, ya gudana ne a Dakin taro na Kwalejin ilimi, wato Kashim Ibrahim College of Education dake Maiduguri.
Taron wanda ya sami halartar wakilin Gwamnan Jihar borno Farfesa Babagana Umara Zulum, wanda kwamishan Matasa da samar da ayyukan yi na Jihar borno, Honarable Sa Inna Buba ya walkita. Sauran Manyan bakin sun hada da, Kwamishan ayyuka na Jihar borno, Honarable Tijjani Bukar, Shugaban bankin kasa (CBN) reshen Jihar borno Dakta Tijjani Lawan kanuriyama, Daraktan kamfanin Bizi Mobile, Dakta Aminu Bizi, Shugaban Kama Integrated Services limited, Kalli Zanna Gambo, Prof. Bello Alhaji Ibrahim
MD/CEO BRMFB LTD, Shugabanin ‘Yan kasuwar Jihar borno, Shugabanin Addinai, Kungiyoyin Matasa da dai sauran su.
A yayin da yake nasa jawabin a madadin Gwamnatin Jihar borno, Honarable Sa Inna Buba, ya jinjina ma kamfanin Bizi Mobile, da hadin gwiwar wadanda suka shirya wannan taro na horar da Matasa akan yadda zasu dogara da kansu.
Honarable Sa Inna Buba, ya bayyana cewa, a shirye Gwamnatin Jihar borno take na ganin sun ci gaba da samarwa da Matasa da ayyukan yi wanda za su ci gaba da dogaro da kansu har su taimaka ma na kasa da su. Ya kuma hori Matasan 270 wadanda suka sami horon akan harkar Agency banking, da su jajirce wajen ganin sun baiwa marada kunya domin su ci gajiyar abin da suka sami horo a kai.
Sabon jin dadi da nuna farin cikin sa, Kwamishan Matasa da samar da ayyukan yi, Honarable Sa Inna Buba, a kashin kansa nan take ya baiwa Matasan gudunmuwar kudi har naira miliyan daya domin kara karfin gwiwa ga Matasan.
Shima a yayin da yake nasa jawabin, Shugaban kamfanin Bizi Mobile Cashless Consultant limited, Dakta Aminu Bizi ya bayyana cewa, a karkashin shirin e-Naira na Babban bankin kasa (CBN) a halin yanzu kamfaninsa ya horar da kuma samarwa da Matasa sama dubu 80,000 ayyukan yi a fadin kasar nan baki daya.
Dakta Aminu Bizi ya kara da bayyana cewa, saboda hazakar da kamfanin ke da shi, tuni Babban bankin kasa na (CBN) ya baiwa kamfaninsa ragamar horar da Matasa akan duk wani abu da ya shafi harkar Agency Banking, shirin e-Naira da dai sauran abin da ya shafi hada hadar kudi irin na zamani.
Suma a nasu jawaban daban daban, Shugabanin kamfanin Kama Integrated services limited, Kalli Zanna Gambo da Prof. Bello Alhaji Ibrahim
MD/CEO BRMFB LTD, sun bayyana shirin na Agency banking da e-Naira a matsayin wani babban gudunmuwar da zasu iya bayarwa na ganin an samarwa da Matasa ayyukan yi, wanda zai hana su zaman kashe wando ko dogaron jiran aiki daga gwamnati.
A yayin da suke zantawa da wakilinmu, Matasan sun nuna godiyarsu ga Gwamnatin Jihar borno, da kuma wadanda suka shirya wannan taro domin horar da su akan yadda zasu dogara da kansu. A cewar Matasan, wannan ba karamin ci gaba ba ne suka samu a tarihin rayuwar su.