Gwamnati Za Ta Kafa Kwamitin Samar Da Hanyoyin Kai Agaji A Arewa Maso Gabas – Sadiya

Gwamnatin Tarayya za ta kafa wani kwamiti na musamman wanda zai samar da hanyoyi mafi sauƙi da za a rinƙa kai agaji ga waɗanda rikicin yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya ya shafa.

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji Da Kyautata Rayuwar Al’umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta bayyana haka a cikin wata takardar bayani ga manema labarai a Abuja ran Litinin.

A cewar ta, rashin samun kaiwa ga jama’ar da rikicin ya shafa wani babban abin damuwa ne.

A takardar, wadda hadimar musamman kan yaɗa labarai ta ministar, Nneka Anibeze, ta rattaba wa hannu, Sadiya Farouq ta ce kula da tsaron lafiyar ma’aikatan agaji a Arewa Maso Gabas shi ma tarnaƙi ne ga aikin kai kayan agaji ga masu buƙata.

Ta ce: “Guruf ɗin ma’aikatan da za a naɗa za su fito da ingantacciyar hanya wadda dukkan mu za mu yi amfani da ita a matsayin ma’aikatan agaji, wanda ya haɗa da jami’an tsaro, saboda mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da juna cikin sauƙi.

“Aikin mu dai na haɗin gwiwa ne, domin kowannen mu ya na buƙatar abokin aikin sa don tabbatar da aikin mu ya cika.

“Don haka, ma’aikatar mu ta na ƙoƙarin ta ga ta kafa wani kwamiti a matakan jihohi da na tarayya wanda zai tabbatar da aikin ya gudana a Arewa Maso Gabas.

“Zai kuma haɗa gwiwa da ma’aikatu da sassan su da cibiyoyin su don ganin aikin raba agaji ya na tafiya yadda ya kamata.”

Ministar ta ƙara da cewa za ta tabbatar da cewa a wurin ma’aikatar ne za a samu duk wani abu da ake buƙata saboda aikin raba agaji ya tafi daidai, ciki har da kai ziyara jefi-jefi a yankin na Arewa Maso Gabas.

Ta ƙara da cewa ma’aikatar za ta riƙa samun rahoton wata-wata ta hannun kodineta mai kula da aikin agaji a yankin (OCHA).

Hajiya Sadiya ta ce za a rinƙa kai kayan abinci da wanda ba na abinci ba zuwa dukkan wuraren da abin ya shafa masu wuyar shiga idan an binciko su.

“Wuraren da za a iya shiga da mota, sojoji ne za su raka mu, yayin da su kuma wuraren da ke lungu sosai za a yi amfani da jiragen Rundunar Sojin Sama ne ana cilla wa mutane kayan agajin zuwa ƙasa inda za su ɗauka.

“Saboda haka, dukkan mu tilas ne mu yi aiki tare da gwamnatocin jihohi, sojoji, Majalisar Ɗinkin NEMA, SEMA da ma wasu don tabbatar da cewa an kai kayan agajin ga mabuƙata.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply