Gwamnati Ta Yi Rawar Gani Wajen Ceto Fasinjojin Jirgi Daga ‘Yan Bindiga – Mai Shiga Tsakani

An bayyana cewar ko shakka babu gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta yi rawar gani wajen ceto dukkanin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da ‘yan bindigar kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa dasu a watannin baya saɓanin yadda jama’a ke tunani.

Sakataren haɗakar kwamitin sulhu tsakanin Gwamnatin tarayya da ‘yan bindigar Farfesa Usman Yusuf ne ya tabbatar da haka a yayin wata ganawa da manema labarai da ya yi a garin Kaduna.

Farfesa Usman Yusuf ya ƙara da cewar tun bayan da ‘yan bindigar suka sace matafiyan cikin watan Maris na farkon shekarar nan, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bai rungume hannu ba ya yi tsayuwar daka domin ganin an ceto dukkanin fasinjojin ba tare da ko guda ya rasa ransa ba.

Dangane da batun ko an biya kuɗin fansa kafin a saki ragowar fasinjojin 23 da ‘yan bindigar suka saka kwanan nan, sakataren kwamitin yace ko kwabo ba a bayar ba, yarjejeniya ce aka yi a tsakanin su da ‘yan bindigar kuma sun cika alkawarin da aka yi saboda haka ba a samu matsala ba.

“Tun farko shawarar da muka ba gwamnati kenan tare da kwamitin da Sheikh Gumi ya jagoranta wajen yin sulhu da ‘yan bindiga a Zamfara, a wancan lokaci ba a amince da shawarar mu ba amma a yanzu gwamnati ta fahimci muhimmancin yin sulhu kuma an samu cigaba akan haka”.

Da aka tambaye shi kan ko me zai ce dangane da zargin da ake yi wa Tukur Mamu wanda ya fara shiga tsakanin yin sulhu da ‘yan bindigar, Farfesa Usman Yusuf ya ce ba zai ce komai akan haka ba saboda a yanzu maganar Tukur Mamu ta na gaban kotu ana bincike, sai dai ya tabbatar da cewa su a ɓangaren kwamitin su ba su amince da batun biyan kudi ba.

Daga ƙarshe ya yi kira ga dukkanin ‘yan Najeriya da su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙar matsalar tsaro domin haƙƙin samar da tsaro lamari ne da ya shafi kowa ba nauyin gwamnati kaɗai ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply