Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Gwamnati Ta Bukaci Jama’a Su Cike Takardun Bayanan Kai Da Kai Daga Bankuna

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya masu asusun ajiye kudade a bankuna ko kamfanonin inshora da su gaggauta karbar takardun cike bayanan kai wato ‘Self-Certification Forms’.

A cewar sanarwar da gwamnatin tarayyar ta fitar ta shafinta na Twitter a ranar Alhamis, ta ce bayan cike takardun, a mayar da su ga bankuna ko kamfanonin ajiye kudaden.

Ga wadanda ke amfani da asusun ajiye kudin a bankuna daban daban, sanarwar ta ce dole su cikewa kowanne banki wadannan takardu, su mayar da takardun ga kowanne banki.

A cewar gwamnatin, bankuna na bukatar wadannan takardu domin yin amfani da su wajen aiwatar da tsare tsare na dokar kudaden shiga daga haraji, doka ta 2019.

Takardun da za a cike, kuma a mayar da su ga bankunan guda uku ne: Takardar bayanin mamallaki (mutum daya), ko kamfani, ko kungiya, da ke da mallakar asusun banki.

Takardar shaidar wakilci (Ga wadanda ke wakiltar mamallakin asusu, misalin amintacce ga mai asusun ko lauyansa, da sauransu).

Takardar cikakken bayanin mutum daya (mamallakin asusun bankin), kamar yadda bayanan suke a lokacin bude asusun bankin.

Gwamnatin ta tabbatar da cewa, “ga duk wanda ya gaza cike wadannan takardu, to zai fuskanci hukunci da ya kama daga cin tara ko kuma garkame masa asusun bankinsa.”

A karshe gwamnati ta bukaci mutane, su tuntubi shafukan hukumar domin neman karin bayani, a shafin twitter @firsNigeria, sai kuma adireshin yanar gizo, http://firs.gov.ng.

Exit mobile version