Gwamnan Babban Banki Zai Gurfana Kotu Yau Laraba

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu jami’an ‘yan sanda sun ziyarci gidan gwamnan babban banki CBN, suna sanya ido saboda wasu manyan dalilai masu karfi.

A cewar rahoton jaridar Punch, wakilin jaridar ya ga jami’ai sama da 10 na sintiri a gidan da misalin karfe 8:40 na dare a ranar Talata. An ga suna ta kai komo ne a gidan gwamnan, Godwin Emefiele mai lamba 8 a titin Colorado da ke Maitama a Abuja.

Wata majiya mai karfi daga hukumar ‘yan sanda ta bayyanawa wakiilin jaridar cewa, sun mamaye gidan ne saboda ana kyautata zaton gwamnan zai bayyana a gaban kotu yau Laraba 18 ga Janairu.

An ce zai bayyana a gaban alkali ne don ba da bahasi kan wasu kudin da suka kai $53m da ke alaka da Paris Club.

Da take bayyana dalilin taruwan ‘yan sandan a gidan gwamnan, majiyar ta ce: “’Yan sandan ba sun zo kama shi bane, sun zo ne don tabbatarwa bai gudu ba kamar yadda ya yi a makwannin baya.”

Sai dai, rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya ta karyata cewa ta tura jami’an don mamaye gidan gwamnan na CBN. Da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sandan birnin, Olumuyiwa Adejob ya ce: “Bani da masaniya game da wannan lamari.

Labarai Makamanta

Leave a Reply