Gwamna Da Shugabantar Boko Haram: Mailafiya Ya Yi Amai Ya Lashe

Bayan amsa gayyatar hukumar jami’an tsaro ta farin kaya, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya, ya janye ikirarin da yayi na farko.

Idan za mu tuna, a wata tattaunawa da aka yi da Mailafiya a wani gidan rediyo na Abuja, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, ya zargi daya daga cikin gwamnonin arewa da zama kwamandan Boko Haram a Najeriya.

A ranar Laraba, kungiyar gwamnonin arewa karkashin gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya kwatanta wannan zargi da babba. Ya ce wannan ikirarin ko dai siyasa ne ko kuma wani yunkurin na sare wa gwamnonin gwiwa duk da kokarin da ake yi na ganin yakar ta’addanci.

A yayin zantawa da manema labarai a garin Jos, bayan amsa tambayoyi da Mailafiya ya yi, ya ce ba a fahimci zantukansa bane. Ya yi mamakin yadda za a yanke masa hukunci a cikin hirar da yayi ta minti 55.

“Tabbas ni na sanar da hakan amma a dukkan hirar minti 55 muka yi. Abinda na fada ne ba a fahimta ba. “Wannan lokacin ba shine na musanta abinda nace ba. Tabbas na fitar da wasu bayanai masu matukar hatsari ga jama’a,” yace. Kamar yadda Mailafiya yace, bayanan da ya tara ya samo su ne daga wasu majiyoyi da bai tabbatar ba.

“Da na yi taka-tsan-tsan wurin tattara bayanan da na samu amma kuma wasu ban nemi karin bayani ba,” ya sanar. Mailafiya ya jinjinawa jami’an tsaro na farin kaya a kan yadda suka karbesa cike da kwarewa da adalci.

A wata takarda da aka fitar a garin Jos, Dr. Mukut Simon Macham, daraktan yada labarai da sadarwa na shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya ce kungiyar gwamnonin arewa ta matukar damuwa da wannan zargi mai girma na Mailafiya, wanda dole ne a bincika da gaggawa.

Takardar ta ce kungiyar, wacce ke aiki tare da gwamnatin tarayya, jami’an tsaro, yankuna, kungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya da na addinai, don kawo karshen ta’addanci a yankin, tana bukatar bincikar ikirarin.

“A matsayin mu na gwamnonin arewa, mun yi taruka babu adadi don tattaunawa a kan rashin tsaron da ya addabi yankin arewa da kasar baki daya. “Muna kushe duk al’amuran ta’addanci kamar Boko Haram, ‘yan bindiga, ‘yan fashi da makami, garkuwa da mutane da sauransu. “Muna saka jami’an tsaro da shugaban kasa don kawo karshen wannan matsalar. “Cewa daya daga cikinmu yana jagorantar Boko Haram a Najeriya babban zargi ne wanda ba za mu bar shi haka ba. Muna bukatar a gaggauta bincike mai tsanani a kai.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply