Da yake yaba wa matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka game da cutar ta COVID-19, Darakta na Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), Dakta Chikwe Ihekweazu ya ce “jihar Kano tana gwajin fiye da kowace jiha a Naieriya. Muna da tabbaci game da sakamakon da suke bamu
Ya yi wanan yabon ne a cikin shirin tashar talabijin ta ‘kasa NTA mai suna Morning Nigeria, inda ya nuna cewa, “akwai wani lokaci a kan wannan shirin da kowa ke sukar Kano game da matakin na yakar cutar Kuma mun tura babbar tawaga zuwa Gwamnatin jihar Kano ta sanya miliyoyin Naira don yaki da cutar Kuma Sun tashi tsaye wajen haka
Ya kara da cewa idan mutane suna tunanin yadda aka tattauna batun Kano wata guda da suka gabata “… da kuma yadda muke magana game da Kano a yau cikin mamaki!
Ya kara da cewa sauran jihohi su dauki darasi daga Kano shugaban hukumar NCDC yace “Hakan na nuna cewa za mu iya juya wannan lamarin a wasu jihohi. Zamu iya juya shi idan muka yi aiki tare. Kuyi aiki tare a fadin tarayya nijeriya da jihohi da za’a samu nasarar yakar cutar
Ya kammala da cewa, “Wannan shi ne abin da na ci gaba da bayarwa. Kowace jiha a Nijeriya ta yin aiki tare don kare lafiyar dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da jihohin da suke zaune ba.”