Rahotannin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar an yi wata arangama tsakanin Kungiyar Boko Haram da tsagen kungiyar karkashin ISWAP.
Rahotanni sun bayyana cewar lamarin fafatawar ya yi sanadiyyar mutuwar manyan kwamandoji daga ?angaren kungiyoyin ta’addan biyu masu gaba da juna.
Majiyarmu ta Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne tsakanin Dikwa da Bama da ke jihar Borno.
Wata majiyar tsaro ta ce Kwamandojin Boko Haram da tawagarsu na kan aikata fashi da makami, lokacin da mayakan ISWAP din a kan babura shida, kowanne dauke da mutum uku suka far musu.
A baya-bayan nan dai ana yawan samun arangama da juna tsakanin kungiyoyin da a baya suka addabi jama’ar yankin da ?asa baki ?aya.