Goron Sallah: Buhari Ya Yi Wasiyya Ga ‘Yan Najeriya Akan Cigaba Da Hakuri

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike Da sakon gaisuwa kan bikin Sallan Layya wanda ake gudanar da bikin a Fadin Duniya baki daya.

Cikin sako daya mi?a kan alamun nasarar aiwatar da bikin ga Al’ummar Musulmai, Shugaban Kasa Ya kara Jaddada kudurin Gwamnatin sa, na Samar da Zama lafiya da yalwan Arziki a ?asar, wacce cikin ta akwai tabbacin gudanar da rayuwa cikin aminci da bada kariya ga Dukiya.

Kan batun kalubalen da a halin yanzu ke fuskantar Kasar, Shugaban Kasa ya bayyana cewa “Annobar Cutar Korona ya kawo Mumunar koma baya ga tattalin arziki na ?asashe, cikin harda Najeriya, wanda hakan ?arine kan yadda ambaliyan ruwa ta janyo lalata lalacewa kayan gona da filayen Noma, wanda hakan ya taka Mumunar rawa gaya a kokarin bun?asa harkan Noma a ?asar wanda hakan yana daidai da Tsarin Gwamnatin mu na ganin an rage shigo da kayakin abinci daga kasashen ?etare.

Yayi jawabin cewa, hakan, yayi sanadin Karuwar Farashin kayan abinci wanda kuma Gwamnati tana nan tana aiki matuka gaya don magance Matsalar.

Bisa ga Shugaban Kasa Buhari, yace “Babu wata Gwamnati nan kusa cikin tarihin mu data zuba jari sosai kamar yadda mukeyi don daga darajan sama da kayakin Masarufi daban daban har guda 20, ta hanyar Samar da bashi da Sauran nau’e nau’en tallafi ga manoma.”

Yace, “baya ga janyo lalacewar gonakin shinkafa da ambaliyan ya janyo, hakanan yan kasuwa sunyi amfani da Wannan damar Gurin gallaza wa ?an-uwa ?an-Nijeriya, don kawo koma baya kan muradin mu na tallafawa da mara baya ga Samar da abinci a cikin gida kan farashi mai Rahusa.

“A Matsayin za?a??en Shugaban ?asa wanda ya samu addu’an Talakawa wanda kuma suka bamu Amanar su, bari na kara tabbatar muku cewa muna cigaba da Daukan Matakai don kawo sauki ga ?an-Nijeriya, ciki harda Samar da takin Zamani cikin Rahusa ga Manoman mu,” Shugaban ya fadiwa ?an-Nijeriya.

Shugaban kasa ya kumayi nuni da cewa rashin tsaro da ake ciki yanzu a ?asar, ya haifar da tsanani da janyo Illoli kan Noma saboda Barayin daji da ?an ta’adda sun hana wasu Manoman damar zuwa gonakin su.”

Shugaban ya kara da cewa “Bari nayi Imfani da wannan dama na kara tabbatar wa ?an-Nijeriya cewa muna nan muna Daukan Matakai don magance kalubalen tsaro, tuni mun fara kawo Jiragen yaki da Sauran kayakin yaki na Soji don inganta aiyukan Jami’an tsaron mu don tunkarar Ta’addanci da Barayin Daji,”

Da yake magana kan Muhimmancin Bikin Ranar Babban Sallah, Shugaban Kasa Yayi roko ga Al’ummar Musulmai” dasu nuna kyawawan dabi’u na addini Musulunci ta hanyar musakai kan nuna hakan a zahirance:

“Suyi Imfani da bikin don amfanuwan Sauran ?an kasa ta hanyar saukaka Farashin kayan abinci da Ragunan Layya kamar yadda koyarwan addinin musulunci yayi

“a Matsayin musulmi mai Imani, kada mu zamanto masu neman riba ta hanyar kuntata rayuwar wasun mu, kada mu nemi jin dadi cikin kukan wasu, a tuna addinin musulunci addini ne na bada sadaka wanda ya umarce mu, da muso makwabcin mu kamar yadda muke son kan mu.

“Ina Umartan dukkan Musulmai da su ci gaba da rayuwa cikin zama lafiya da kwanciyar hankali da Sauran ?an-Nijeriya dake wasu addinai daban tare da ruhin Dabbaka zama lafiya. A ko wani lokaci muyi Addu’a don Cigaban Najeriya. Mu tona Asirin duk wani fasa gurbi dake cikin mu wanda suke kawo rashin zama lafiya ga ?asar Mu.”

Mal. Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a.
19 ga watan Yuni, 2021

Related posts

Leave a Comment