Gombe: ‘Yan Mata Sun Koka Rashin Mazan Aure

A wani lamari mai kama da wasan kwaikwayo, wasu mata marasa Aure a jihar Gombe sun yi kukan neman taimako kan rashin samun mazajen aure, kamar yadda Jaridar The Nation ta ruwaito

Wannan mummunan lamarin ya ci gaba tsawon wasu shekaru a yankin Arewa maso yammacin kasar, inda ta kara da cewa daruruwan mata marasa aure karkashin jagorancin Suwaiba Isa sun mamaye jihar Zamfara.

Sun yi hakan ne don zanga-zangar rashin samun mazajen Aure ga kimanin su 8,000 a watan Satumban 2018.

Manema labarai sun tattaro cewa sarkin Yarbawa a Gombe, Abdulrahim Alao Yusuf, ya ce kashi 60% na mutanen da ba ‘yan asalin jihar bane sun fito ne daga yankin kudu maso yammacin kasar.

Daya daga cikin mazauna jihar Gombe, Godiya Adamu, ta ce shekarunta 35, har yanzu ba ta samu miji ba, tana mai dora alhakin halin da ake ciki kan rashin samun namijin da ke son aure da gaske.

Ta bayyana cewa ta yi soyayya na kimanin shekaru biyar ba tare da sakamako mai ma’ana ba kafin daga baya ta hakura.

Wata Bafulatana, mai suna Amina, ta ce matsalarta ita ce ta yi karatu, tana mai cewa ta gano cewa yawancin maza a arewa ba sa son auren mata masu ilimi.

“Wataƙila saboda suna ganin ba abu mai sauƙi ba ne a gare su su juya irin wannan matar son ransu. Don haka a wurina, zaɓin shi ne na ci gaba da zama ba aure sannan na zamo uwa da uba ga yarana.”

A nasa jawabin, Babban Limamin Masallacin gidan Gwamnati a Gombe, Sheik Dr. Zakariya Hajiya, ya dora alhakin rashin samun mazajen da mata bas a yi a jihar kan talauci.

Labarai Makamanta

Leave a Reply