Gombe: Ta Kashe Kanta Dalilin Auren Dole

Wata budurwa yar asalin jihar Gombe mai suna Amina Isah Kuma mazauniyar unguwar Bamusa takashe kanta saka makon auren dole da iyayenta suka mata.

Kamar yadda Wakilin mu ya tattauna da Wata kawarta ta bayyana mana mana Cewa, ita Amina tana soyayyane da wani wanda takeso mai Suna Muhammad, daga bisani kuma iyayenta suka tilasta mata auren wani Wadda bata son sa wadda hakan yakai ga iyayenta sun aura mata wanda suke so alhali kuma ita bata son shi.

Kafin dai budurwar tasha madarar fiya-fiya tamutu tayiwa wasu daga cikin kawayenta
Text Massage Wadda suka hada da Hassana, Zahra, Da Aisha, akan cewa itafa muddin aka mata auren dole to wlh zata kashe kanta.

Haka kuma tasanarda mahaifinta Malam Isa cewa itafa muddin aka aura mata wanda bataso sai ta kashe kanta, budan bakin mahaifin ta sai yace takashe mana idan hauka takeyi, yarinyar dai kafin gari ya waye tasha fiya fiya ta mutu har lahaira.

Muna fatan hakan zaizama izina ga sauran iyaye dasu keyiwa wajen yiwa yaran su auren dole.

Labarai Makamanta

Leave a Reply