Kotun Majistare a jihar Gombe ta tsare wani Matashi mai suna Khalid Abdallah mai shekaru, 25, a gidan gyaran hali saboda zagin wani dan majalisar jihar a dandalin sada zumunta ta Facebook.
Wanda ake zargin mazaunin Kashere a karamar hukumar Akko a jihar Gombe ya yi amfani da shafinsa na Facebbok ya rubuta kalaman batanci ga dan majalisa mai wakiltan Akko ta Yamma a majalisar jihar, Abdullahi Abubakar.
Kamar yadda rahoton da ‘yan sanda suka karanto wa wanda ake zargin a lokacin da ya gurfana a kotu ya nuna, a ranakun 10, 11, 14 da 19 na watan Satumba wanda ake zargin ya wallafa a shafinsa cewa dan majalisar dan luwadi ne, jahili kuma makaryaci.
Dan sanda mai shigar da kara, Habibu Danjuma Juwara ya sanar da kotun cewa wannan rubutun karya ne kuma da gangan aka yi don cin mutuncin wanda ya yi karar duk da cewa wanda ya hallafa ya san rubutun zai bata wa dan majalisar suna.
Mai shigar da karar ya ce hakan ya saba wa sashi na 393 da 399 na dokar Penal Code. Wanda ake zargin ya musanta zargin ya kuma nemi beli ta hannun lauyansa Barrister Saidu Muazu Kumo.
Juwara ya ki amince da bada belin inda ya ce wanda ake zargin zai iya kawo cikas ga binciken.
Alkalin kotu Japhet Maida ya bada belin wanda ake zargin amma sai ya kawo mutum biyu da za su tsaya masa ciki har da Hakimin Kashere.
Wanda ake zargin ya gaza cika ka’idojin belin hakan yasa kotu ta bada umurnin a ajiye shi a gidan gyaran hali.
An daga cigaba da shari’ar zuwa ranar Laraba 14 ga watan Oktoba.