Gwamnatin Nijeriya ta tallawa matashin da ya yi azumi bakwai domin Allah ya kawo karshen mulkin jam’iyyar APC da zunzurutun kudi har Naira 200,000.
Idan baku manta ba a kwanakin baya Jaridu sun wallafa labarin dan kasuwa Musa Sulaiman Sarki, dake jihar Gombe ya gabatar da Addu’a tare da Azumi har guda Bakwai domin Allah ya kawo karshen mulkin Jam’iyyar APC a fadin kasar.
Gwamnatin Nijeriya ta tallafawa matashin ne tare da sauran Abokanan kasuwancin shi, a karkashin tsarin tallafin farfado da tattalin arzkin ‘yan Nijeriya, wanda cutar Corona tayi sanadin karyewar tattalin arzkin al’ummar kasar, har al’umma da yawa suka rasa jarin da zasu yi kasuwanci dashi.
Haka zalika matashin ya jinjinawa gwamnatin shugaba Buhari kan yadda take tallafawa al’umma marassa karfi da jari domin su dogara da kansu.