Gombe: An Yi Jan Hankali Kan Jan Ruwa Ta Ɓarauniyar Hanya

Rahotanni daga Jihar Gombe na bayyana cewar an yi jan hankali ga masu ruwa da tsaki a Gombe da cewa su kara jajircewa wurin ganin an kawo karshen jan ruwa ta haramtattiyar hanya daga babban bututun daya ke samar da ruwa a garin Gombe da kewaye daga matatar ruwa na Dadin Kowa.

Kwamishinan ruwa na jihar Gombe Alhaji Mijinyawa Yahaya ne yayi Jan kunnen yayin da yake magana da manema labaru a ofishin sa dangane da jan ruwa ta haramtattiyar hanya daga Babban bututun ruwa daya ke samar da ruwa a garin Gomben daga matatar ruwa na Dadin Kowa.

Mijin Yawa ya ƙara da cewa hakan yana yin mummunar tasiri wurin samar da ruwa kuma a cewar shi masu ruwa da tsaki nada gagarumar rawar takawa wurin magance matsalar ka da ta gagari kundila.

Yace abin takaici ne matuka duk da makudan kudade da gwamnatin jihar ke kashewa wurin samar da ruwa amma sai gashi wasu mutane suna yin kafar angulu a wannan kokarin dake da manufar kawo wa jama’a saukin rayuwa.

Alhaji Mijinyawa Yahaya ya kara da cewa an gyara wasu tsaffin rijiyoyin burtsatse a garin Gomben domin su dafawa madatsar ruwa na Dadin Kowa a ko da yaushe a ringa Samar da ruwa ga jama’a.

Bayanan da wakilin muryar yanchi na Gombe Muhammad Ibrahim Pantami ya tattara sun baiyana cewa a yanzu ana samun ruwa a garin na Gombe lamarin dake tabbatar da cewar gwamnatin jihar tana yin abun daya dace a bangaren samar ruwan wanda yan magana ke cewa abokin aiki kuma ruwa abokin rayuwa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply