Gombe: An Raba Tallafi Ga Wa?anda Rikicin ?illiri Ya Shafa

A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan watsa labaru na Gidan Gwamnatin jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli, an gudanar da aikin raba kayan ne ta hannun kwamiti na musamman da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya kafa domin tabbatar da raba kayan bisa gaskiya da adalci.

Da yake zantawa da manema labarai yayin rabon kayan a garin Billiri, Shugaban kwamitin, wanda kuma shi ne Kwamishinan kananan hukumomi da lamuran masarautu, Hon. Ibrahim Dasuki Jalo ya ce kimanin mutane 2000 ne suka ci gajiyar 2000 kayan tallafin, inda ya ce kafa kwamitin rabon kayayyakin agajin da Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya yi ya biyo bayan barnata dukiyar wasu mazauna garin da ba su ji ba su gani ba yayin rikicin wanda ya samo asali akan nadin sabon Mai Tangle.

Dasuki yace “Mai Girma Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya cikin hikimarsa ya ga bukatar kawo tallafi ga wadanda rikicin ya rutsa da su a garin na Billiri ta hanyar samar da wadannan kayan agaji kafun zuwa lokacin da kwamitin da aka kafa ya kammala aikin sa na tattara bayanan yadda za a biya diyya.

Wasu da suka ci gajiyar tallafin wadanda suka yi magana da manema labarai yayin jimkadan bayan kammala rabon kayan, sun nuna farin cikinsu da godiyar su ga gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya game da kawo musu dauki.

Taron rabon kayan wanda aka gudanar a filin wasa na garin Billiri an gudanar da shi ne karkashin kulawar mambobin kwamitin, jami’an karamar hukumar ta Billiri da kuma jami’an tsaro.

Membobin kwamitin na Dasuki Jalo Waziri sun hada da Kwamishinan ayyuka na musamman, Christopher Abdu Buba Maisheru, mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro, Col Sani Adamu Dapsia (Rtd), Shugaban karamar hukumar Billiri, Margaret Bitrus da Shugaban APC, karamar hukumar Billiri.

Sauran sun hada da Darakta-Janar / Kodinetan Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas, NEDC a jihar Gombe, Shehu Yarima Abdullahi da Misis Eglah Idris yayin da Babban Sakatare mai zaman kansa na Gwamnatin jiha, Malam Usman Kamara yake a matsayin Sakatare.

Related posts

Leave a Comment