Gwamnatin Jihar Gombe ?ar?ashin jagorancin Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ta nada sabon Sarkin Masarautar Tangale Mai Tangale.
Wanda aka na?a shine Alhaji Muhammad ?anladi Sanusi Maiyamba a wannan rana ta Laraba. Ana sa ran na?in nashi za a kawo karshen takaddamar da ta biyo bayan kan sarautar gargajiya ta Mai Tangale a garin Billiri dake jihar Gombe.
Kwamishina, a Ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin Masarauta na jihar Alhaji Ibrahim Jalo ya sanar da hakan tare da amincewar Gwamnan sannan aka gabatar da nadin daga sabon Mai Tangle a Poshiya dake Billiri.
Ya ce nadin Sunusi Maiyamba ya tabbata ne ta hanyar duba da halayensa da dacewarsa. Bikin gabatarwar ya samu halartar Shugaban karamar hukumar Billiri, Sarakuna tara na masarautar Billiri, mambobin majalisar gargajiya da sauran masu rike da mukamai.
Mai Tangale na 15, Abdu Maisharu II, ya mutu yana da shekaru 72 bayan gajeriyar rashin lafiya. Biyo bayan mutuwar sarkin, rikici ya balle tare da nuna rashin amincewar kiristocin yankin na nada sabon sarkin da zai kasance musulmi.
An kashe mutane uku tare da lalata dukiya ta miliyoyin nairori a karamar hukumar Billiri ta jihar Gombe yayin da rikici kan nadin sabon Mai Tangale ta yi kamari a kwanakin baya.