GOMBE 2023: Mailantarki Kwashe Baraden Yakin Isyaku Gwamna, Sun Koma NNPP

Daga Wakilin Mu

Ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe a jam’iyyar NNPP, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya na ci gaba da karɓar dandazon manya da ƙananan magoya bayan APC mai mulkin jihar da kuma PDP.

A ƙarshen makon nan ne Mailantarki ya haska wa wasu manyan mambobin PDP hanya, su ka bi ta gwadaben da su ka koma NNPP.

Mambobin dai zaratan magoya bayan fitaccen ɗan siyasar nan ne Jamil Isyaku Gwamna, waɗanda ake kiran ƙungiyar su da suna Sardauna Dawo-Dawo.

A ranar Juma’a ce Mailantarki ya karɓi dandazon ‘yan PDP ɗin a bisa tarbar su da Shugaban NNPP na Jihar Gombe ya yi, wato Alhaji Abdulahi Maikano.

Wannan dandazon magoya baya dai sun canja sunan su daga Sardauna Dawo-Dawo zuwa Mailantarki Movement, bayan sauya sheƙar su daga PDP zuwa NNPP.

Sun bayyana cewa sun yanke shawarar goyon bayan ɗan takarar da “matashi ne mai jini a jika, wanda ke da jama’a a kowane ɓangaren al’umma, nagari na kowa, ƙwararre, kuma mai zuciyar tausayin al’umma.”

Shugaban tawagar mai suna Muhammad Makson ya bayyana cewa Gombawa ba su da wata matsala da Mailantarki, domin an jaraba shi a baya, kuma ya ci jarabawar riƙon amanar da aka damƙa masa.

“A kan haka, Mailantarki na da gogewar da zai iya magancewa da shawo kan matsalolin da su ka dabaibaye jihar Gombe.

“Gaba ɗayan mu ne mu ka yi shawarar ficewa daga PDP mu ka yanke shawarar dawowa cikin NNPP, saboda buƙatar ganin mun samu nagartaccen shugabancin da ya fi dacewa da Jihar Gombe.

“Mun yi amanna cewa Mailantarki ne zai iya tsamo Jihar Gombe daga kwazazzabon ramin da APC ta jefa jihar, sakamakon tuƙin gangancin da ake yi da motar da APC ta cika da lodin al’ummar Gombe.”

Makson ya ce waɗanda su ka fice daga PDP ɗin zuwa NNPP akwai shugabanni 2000, mambobi sama da 20,000 a faɗin mazaɓu 114 na Jihar Gombe.

Mailantarki ya tabbatar masu da cewa shi da NNPP za su tafi tare da su domin a gudu tare, a yi nasarar kafa gwamnati tare.

Daga nan ya roƙesu cewa sai sun ƙara tashi tsaye sosai wajen yaɗa manufofin NNPP da tallata ‘yan takarar jam’iyyar a cikin yankunan karkara, ta yadda za a kawar da gwamnatin APC a ranar zaɓen 2023.

Labarai Makamanta

Leave a Reply