Gobarar Kasuwar Sokoto: Gwamnan Kebbi Ya Bada Gudummuwar Miliyoyi

Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya kai ziyarar jaje ga Gwamnatin jihar Sokoto sanadiyar gobarar da ta kone sabuwar Kasuwar garin Sokoto, inda ya samu tarbo daga takwararsa Gwamnan Jihar Sokoto Rd. Hon. Aminu Waziri Tambuwal.

Haka zalika Gwamna Bagudu ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kebbi ta bada gudummuwar maira milyan talatin ( 30,000000).

A nasa bangaren, Gwamna Tambuwal ya yi godiya ga Gwamna Bagudu bisa wannan gudummuwa da Jihar Kebbi ta baiwa ‘yan kasuwar Jihar Sokoto da Iftila’in gobara da ya shafi Yan Kasuwar Jihar Sokoto inda Gwamnan Jihar Sokoto ya bayyana cewa Jihar Kebbi ita ce Jiha ta farko da ta kawowa wadannan yan kasuwa Gudummuwa saboda jihar Kebbi da jihar Sokoto uwa da uba daya suke.

Daga karshe Gwamnan Bagudu ya yi addu’ar Allah ya maidawa ‘yan kasuwar da alheri.

Daga Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi.

Labarai Makamanta