Gobara Ta Hallaka Wata Daliba A Jami’ar Jihar Yobe

IMG 20240324 WA0045

Allah ya yiwa wata dalibar jami’ar tarayya da ke Gashua (FUGA) mai suna Shamsiyya Murtala rasuwa bayan tashin gobara a dakin kwanan dalibai a jami’ar.

Wannan mummunan lamarin ya auku ne a ranar Asabar 23 ga watan Maris na wannan shekarar, kamar yadda rahoto ya bayyana.Wutar ta kama ne a dakin kwanan dalibai a lokacin da dalibar ke barci mai nauyi.

An ruwaito cewa, sauran dalibai sun yi kokarin ceto ta daga wutar, amma suka gaza fasa kofar dakin don samun damar shiga.

Asibitin kwararru na Gashua ne ya tabbatar da mutuwarta bayan da aka tattara ta zuwa asibitin bayan bude kofar. Wutar dai an ce ta yi barna a bangarori daban-daban na dakin kwanan daliban mata, musamman kadarori masu amfani kuma masu daraja.

Majiya ta bayyana cewa, wutar ta kama ne da misalin karfe 10 na safe a ranar Asabar 23 ga watan Maris a daidai lokacin da daliban ke kan harkokin karatunsu. Rundunar kashe gobara ta jami’ar da ta jiha sun kawo dauki, inda suka yi nasarar kashe wutar cikin gaggawa.

 

Labarai Makamanta

Leave a Reply