Shugaban Kungiyar JIBWIS, kuma shugaban gamayyar kungiyoyin Ahlussunnah ta Afirka, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufa’i, da ya dau matakin gaggawa akan ‘yan garkuwa da mutane, musamman akan hanyar kaduna zuwa Abuja, da sauran hanyoyin jihar baki daya.
Sheikh Bala Lau a jawabinsa a dakin taro na na gidan gwamnatin jihar, a wata ziyara da kungiyar ta kai masa, ya bayyana makasudin ziyarar cewa sun kawo ziyarar ne domin bada shawari kan matsalar tsaro daya addabi jihar, kama daga matsalar fadace-fadace a kudancin jihar da kuma garkuwa da mutane akan babban hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Sheikh Bala Lau ya kara da cewa, lallai wajibine shugabanni su san cewa babban hakkin da ya rataya akansu shine bada tsaro ga rayuka da dukiyoyin al’umma. Don haka, duk da cewa gwamnanti tana iya kokarinta, lallai ya zama wajibi a kara kokari domin shawo kan wannan masala.
Shima a nasa jawabin, Gwamna jihar Nasiru Elrufa’i ya bayyana matukar farin cikinsa kan wannan ziyara, sannan ya baiyana wa tawagar cewa tsawon shekaru biyar daya kwashe a gidan gwamnatin jihar Kaduna bai taba karban Manyan malamai irin na yau ba.
Har ila yau, gomnan ya bayyana wa shugaban cewa a shirye suke ko wani lokaci su karbi shawarwari daga shuwagabannin addini don magance rikicin addini daya addabi jihar.
Ya kuma ce ana daukan matakai, kuma zasu kara daukar matakan akan tsaro cikin ikon Allah.
Jibwis Nigeria