Garba Shehu Bai San Aikinsa Ba – Dattawan Najeriya

Dattawa masu kishin Nijeriya sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori mai taimaka masa ta fuskar yada labarai Garba Shehu, saboda zarginsa da suke na rashin tauna magana kafin ya fade ta.

Wannan kira ya zo ne bayan wata magana da Shehun ya yi, inda yake ikirarin cewa Shugaban kasa ne kadai ke da ikon kayyade wa’adin shugabannin tsaron kasar.

Da yake magana kan kin sauke hafsoshin tsaron da Buhari bai yi ba lokacin da ake fira da shi a wani gidan talabijin, Garba Shehu ya ce babu wani sashe a kundin tsarin mulkin kasar da ya kayyada wa’adin da hafsoshin tsaron za su yi.

Saidai kuma dattawan, cikin wata sanarwa hadin guiwa da ta samu sa hannun Prof. Tunde Banjo, Dr Achike Nwachukwu, Barr. Jackson Spiff, Alhaji Baba Usman Funtua, Prof. Shehu Bulama da Dr. Isaiah Terhila sun gargadi kakakin shugaban kasar da kar ya janyo wa kan sa abun da zai sa fushin ‘yan Nijeriya ya kare kan sa, dangane da halin matsalar tsaron da kasar ke ciki.

Labarai Makamanta