Ganin Likita: Ba Dole Bane Buhari Ya Mika Mulki Ga Osinbajo – Fadar Shugaban Kasa


Fadar Shugaban kasa ta fito fili ta yi ?arin haske dangane da surutan da jama’a ke yi akan wajabci ko rashin wajabcin shugaban ?asa Buhari ya mi?a mulki ga mataimakinshi Osinbajo a yayin tafiya ganin likita, inda ta bayyana cewar ba dole bane shugaban ya yi haka.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya bayyana hakan a ranar Talata lokacin da ya bayyana a matsayin bako a shirin Politics Today na gidan talbijin din Channels.

Ya yi bayanin cewa Shugaba Buhari bai sabawa dokokin kasar ba ta hanyar kin mika ragamar mulki ga Farfesa Osinbajo yayin da ya bar kasar na wasu kwanaki.

“Shi (Buhari) zai ci gaba daga duk inda yake,” in ji Shehu lokacin da aka tambaye shi ko Shugaban kasar ya mika ragamar ayyuka ga mataimakin shugaban.

Ya kara da cewa, “Abin da doka ta tanada shi ne cewa Shugaban kasar zai kasance ba ya cikin kasar har na tsawon kwanaki 21 da fiye da haka, to a kan hakan ne ake da garantin mika mulki. A wannan yanayin na musamman, ba bu bukatar haka.”

Yan sa’o’i kafin tattaunawar, Shugaba Buhari ya tashi daga Fadar Shugaban Kasa zuwa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 2:30 na rana inda daga nan ya wuce zuwa Landan don duba lafiyarsa.

Related posts

Leave a Comment