Shugaban dakarun sojojin kasan Najeriya, Laftana Janar Tukur Buratai, cikin fushi ya mayar da martani ga masu ƙorafin cewa Shugabannin tsaro sun gaza a sallame su, inda yace masu irin wannan ƙorafi wasu jama’a ne da suka jahilci yadda ayyukan tsaro suke.
Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi wannan magana ne a shafinsa na Facebook, ya na nuna cewa yanzu aka fara yaki da miyagu, kuma ganin bayan su gaba ɗaya sai wanda Allah ya azurta da tsawon rai zai gani.
Shugaban dakarun Sojin ya kara cewa fadan da ake yi da ‘yan ta’adda da masu tada zaune-tsaye, zai iya kai akalla wasu shekaru 20 masu zuwa nan gaba.
“Jama’a sun yi tarayya wajen rashin fahimtar abin da yakin sunkuru da ta’addanci ya kunsa. Akwai yiwuwar a kara shekaru 20 ana fama da ta’addanci.”
“Ya danganta ne da yadda abin ya rincabe da kuma martanin da duk wasu masu ruwa da tsaki suke yi; jami’an sojoji da kuma farar hula, dole ‘yan Najeriya da “yan ƙasar waje su bada gudumuwarsu a yakin.
“Akwai matukar bukata da tasirin al’umma. Dole duk su hada kai wajen shawo kan sha’anin rashin tsaron da ya ki ci, ya ki cinyewa.”
Janar Tukur Buratai ya ƙara da kiran cewa dole kowa ya tashi tsaye, a kawo karshen matsalar.