Ganduje Ya Kori Kwamishinan Harkokin Addini Baba Impossible

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kori Kwamishinan Horkokin Addini, Dakta Muhammad Tahar Adam, wanda a ka fi sani da Baba Impossible.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da Muhammad Garba, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin gida da ya fitar a yau Asabar a Kano.

A sanarwar, Garba ya ce korar ta nan-take ce.

Ya ƙara da cewa korar ta biyo bayan wasu halaye marasa kyau da Baba Impossible ke nunawa a matsayin sa na mai riƙe da ofishin gwamnati, inda ya ƙara da cewa kalaman rashin kan-gado da ya ke furtawa na cikin dalilan da ya sa Ganduje ya saita wa Kwamishinan hanya.

A cewar Garba, an gano cewa Baba Impossible na gudanar da harkokin ofishinsa a matsayin wani kasuwanci sannan kuma ya rage ranakun zuwa ofis na ranaku biyu, Laraba da Juma’a.

Malam Garba ya ƙara da cewa bayan laifin gudanar da ofishin sa ba tare da tuntuɓa ba, Baba Impossible ba ya biyayya ga Gwamna Ganduje.

Ya ƙara da cewa tuni gwamnan ya aike da sunan Dakta Nazifi Ishaq Bichi zuwa ga majalisar dokokin Kano domin tantance shi ya maye gurbin Baba Impossible.

Sai dai a martanin da ya mayar tsohon Kwamishina Baba Impossible ya bayyana cewar ba korar shi Ganduje ya yi ba shi da kanshi ya ajiye aikin don raɓin kanshi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply