Ganduje Na Samun Turjiya A Yunkurin Darewa Shugabancin APC

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa akwai alamu mai karfi da ke nuna wasu ‘yan majalisar gudanarwa ta NWC na jam’iyyar APC, ba su yi amanna da Abdullahi Umar Ganduje ba a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC.

Daga cikin korafin da ake yi shi ne tsohon Gwamnan mai shekaru 73 ya fito daga jihar Kano ne, alhali Arewa maso tsakiya ta ke rike da shugabanci. Wata majiya da ke kusa da Abdullahi Ganduje wanda ya yi shekaru takwas yana Gwamna a Kano ta ce an dauko shi ne saboda biyayya da amanarsa.

An rawaito Mataimakin shugaban APC a Kudu, Emma Eneukwu ya na cewa maganar nada tsohon Gwamnan ya zama shugaban jam’iyya rade-radi ne. Eneukwu yake cewa jita-jita ce kurum ke yawo cewa Ganduje zai karbi shugabancin jam’iyyar APC, ya ce ba zai iya magana kan abin da bai tabbata ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply