?an jaridan da ya fitar da jerin bidiyon da ke zargin Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kar?ar cin hanci ya ce ya bar Nijeriya ne saboda ba shi da ?warin gwiwar hukumomi za su kare rayuwarsa.
Cikin hirarasa da BBC Hausa daga Ingila, Ja’afar Ja’afar ya ce zai ci gaba da neman mafaka a Birtaniya tare da iyalinsa har sai ya samu tabbacin za a kare rauywarsa idan ya koma Najeriya.
Kazalika, ya yi zargin cewa cin hanci da rashawa a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari sun ?ara ta’azzara, inda ake ya?ar masu fallasa bada?alar maimakon ainihin masu aikata cin hancin.
A shekrar 2018 ne mawallafin jaridar Daily Nigerian ?in ya saki wasu bidiyo da ke zargin cewa Gwamna Ganduje ne yake kar?ar damman daloli daga hannun wani ?an kwangila a matsayin cin hanci.
Sai dai gwamnan ya sha musanta zargin yana mai cewa ?ir?irar bidiyon aka yi.