Ganawar Buhari Da Tsoffin Shugabanni: Ba Zan Saurara Wa ‘Yan Ta’adda Ba

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba zai rungume hannu ba yana kallon ‘yan ta’adda suna cin karensu babu babbaka ba a Najeriya, ya zama farali gareshi ya tashi tsaye ya yi maganin duk wani ?an Ta’adda a Najeriya.

Buhari ya fadi hakan ne a taron da yayi da tsofaffin shugabannin kasa, su Janar Yakubu Gowon, Olusegun Obasanjo, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Ernest Shonekan, janar Abdulsalami Abubakar da Goodluck Jonathan, a fadar Shugaban ?asa.

Shugaban kasa yace abin kaico ne ace daga manufar matasa ta rushe rundunar SARS ta koma tashin hankali da rikici da ke neman ?allewa na ?abilanci da addini.

Ya ce asalin abinda ya janyo zanga-zangar shi ne kama-karyar da wasu daga cikin ‘yan rundunar SARS ke yi, wanda suka bukaci a rushe rundunar kuma aka yi. Shugaban kasa yace, “Mun amince da bukatunsu amma sun cigaba da zanga-zangar wacce ta janyo zubar da jini.”

Kamar yadda kakakin shugaban kasar ya ce a wata takarda, abinda ya fi tada masa hankali shine kashe-kashe da asarorin dukiyoyin gwamnati da na al’umma.

Shugaban kasa ya roki ‘yan Najeriya a ranar Alhamis, inda yace “Za mu cigaba da inganta mulki don samar da rayuwa mai kyau ga ‘yan kasa. “Za mu cigaba da tabbatar da bai wa matasa dama, taimakon ‘yan Najeriya da basu ‘yancin su. Zamu cigaba da tabbatar da hadin kan ‘yan kasa,” cewar shugaban kasa.

Related posts

Leave a Comment