Ganawa Da Tinubu: Kungiyar Kwadago Ta Janye Shiga Yajin Aiki

Gamayyar ƙungiyar kwadago ta kasa NLC ta dakatar da shiga yajin aikin da ta shirya gudanarwar a fadin ƙasar sakamakon cire tallafin man fetur.

Shugaban haɗaɗdiyar ƙungiyar ƙwadago ta TUC Festus Osifo ne ya bayyana haka lokacin wata tattaunawa da gidan talbijin na Arise News da safiyar ranar Alhamis.

Ya ce sun ɗauki matakin ne bayan ganawar da shugabbannin ƙungiyar suka yi da shugaban ƙasa Bola Tinubu, wanda ya nuna zai duba buƙatun ƙungiyar tare da ɗaukar matakai cikin gaggawa.

Kan haka ne ya ce ƙungiyar ta dakatar da gudanar da yajin aikin da ta shirya gudanarwa a ranar Alhamis.

A ranar Laraba ne dai ƙungiyar ta fara gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar domin nuna ɓacin ranta kan matakin cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

A nata ɓangare fadar shugaban Najeriya ta fitar da wata sanarwa cikin daren Laraba, inda a ciki take bayyana irin ci gaban da ta ce an samu sakamakon ganawar shugabannin ƙungiyar ƙwadagon da kuma shugaban ƙasar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.

Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban zai yi nazari game da buƙatun da shugabannin ƙungiyar suka gabatar masa a lokacin ganawar, domin dakatar da zanga-zangar da ƙungiyar ke fara gudanarwa a ranar Laraba.

Shugaba Tinubu ya tabbatar wa ƙungiyar ƙwadagon cewa matatun mai ta Fatakwal za su fara aiki, nan da watan Disamba mai zuwa, bayan kammala aikin gyara su, da kamfanin mai na ƙasar NNPCL tare da haɗin gwiwar kamfanin Maire Tecnimont SpA na Italiya.

Sanarwar ta kuma ambato shugaban ƙasar na tabbatar wa shugabannin ƙungiyar cewa zai ci gaba da aiki domin ciyar da ƙasar gaba, sannan kuma ya yi kira ga shugabanin da su haɗa hannu da shi domin samar wa ƙasar yanayin tattalin arziki mai inganci.

Labarai Makamanta

Leave a Reply